MDD, ta sanar da shirin tsagaita buda wuta na Sa’o’I 72 a kasar Yemen, wace za ta soma aiki daga ranar Alhamis mai zuwa.
Majalisar ta sanar da hakan ne bayan Shugaban kasar ta Yemen mai murabus Abdel-Rabbo Mansur Hadi dake tsugunne a Saudiyya ya amince a tsaigata wuta a jiya Litinni, kwana guda bayan kiran da kasashen duniya suka yi kan wannan bukata.
Jakadan Majalisar na musamman a Yemen, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ce ya tuntubi ‘yan gwagwarmaya neman sauyi na kasar ta Yemen wato ‘yan Huthi inda suma suka amunce da wannan bukata.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi maraba da wannan shirin tare da bukatar da a kara tsawaita shirin bayan kwanaki ukun, don neman hanyar kawo karshan yakin basasa a Yemen.
Wannan dai na zuwa kwanaki kadan bayan kazamin harin da Saudiyya ta kai kan wani zamen makoki a birnin Sanaa inda mutane sama da 140 suka rasa rayukansu.
Rikicin kasar Yemen dai ya lakume rayuka mutane kimanin 7,000 da jikkata sama da 35,000, bayan miliyoyi da ya tilastawa gudun hijira tun daga watan Maris din shekarar da ta gabata a cewa Majalisar Dinkin Duniya.