Sanarwa ta musamman daga Kungiyar ‘Yan Kasuwar Turkiyya ga ‘yan Najeriya


 

 

A matsayinmu na mambobin Kungiyar ‘Yan kasuwa da masu Masana’antu Masu Zaman Kansu na Turkiyya MUSIAD ya zama dole mu sanar da ‘yan Najeriya musamman ma abokan huldarmu kan wasu abubuwa masu muhimmanci kamar haka:

Muna sane da cewa, kungiyar ta’adda ta FETO ta yi yunkurin juyin mülki a a Turkiyya a ranar 15 ga watan Yuli wanda kuma ba ta yi nasara ba. Sakamakon haka an samu zanga-zanga da dama a ciki da wajen Turkiyya. Kuma zanga-zangar da muka yi a Abuja na da muhimmanci kuma an yi ta lami lafiya. A saboda haka muke so mu bayyana muku wasu abubuwa.

Sanin kowa ne cewa, wannan kungiya ta ta’adda na da kadarori sosai a Najeriya. Su ne suke da Asibitin Nizamiye, Jami’ar Nile University da kuma makarantun Nigerian Turkish Colleges. Sun zo Najeriya da sunan suna taimakon ‘yan uwanmu Musulmi, amma kuma gaskiyar abin shi ne su samu damar kafa makarantunsu masu tsadar gaske, tare da tsururutar talakawa da shiga madafin iko suna tallafawa ‘ya’yansu da damar yin karatu kyauta wanda hakan ke dakile cigaban talaka. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayar da umarni cewa, a mayar da dukkanin kadarorin wannan kungiya su zama mallakar gwamnati Najeriya. Hakan zai bayar da damar rufe hanyoyin danne hakkin yara kanana.

Ma’aikatar Ilimi ta Turkiyya a shirye ta ke da ta hada kai da hukumomin Najeriya don karbe wadannan makarantu wanda hakan zai taimaki marasa galihu. Manufar hakan shi ne, duk kudaden da za a sam uza a yi amfani da su a Najeriya wajen bunkasa ilimin kasar.

An yi irin wannan bincike tare da karbe makarantun kungiyar a wasu kasashe 16 bayan umarnin da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya bayar, inda wasu kasashen 11 suka bayar da sanarwar fara yin wannan abu.

Kamar yadda shugabanmu Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana, wannan kungiya ta FETO ba ta da bambanci da ‘yan ta’addar Boko Haram, Daesh, PKK da Alqa’eda, wadanda kuma suke ikirarin mallakar jami’an leken asiri a kasashen waje don yakar kasarsu. Sakamakon haka muke kira ga gwamnatin Najeriya musamman ma Mai Girma shugaban kasa Muhammadu Buhari mai gasikiya da dalci da ya shiga wannan magana don dakatar da ‘yan kungişyar ta’adda daga kulla-kullar da suke yi wadda ke lahani ga tsarin Najeriya.

Muna jiran yin aiki tare da ‘yan Najeriya masu girma a koyaushe.

Maana Plaza 38 Douala Crescent, Wuse Zone 5 FCT Abuja, Nigeria.

Lambobin waya: +234 80 6020 7744 / +234 70 6052 2807

www.musiad.org.ng

You may also like