Sanata Ali Wakil ya mutu


Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta kudu a majalisar wakilai, Malam Ali Wakili ya mutu yana da shekaru 58.

Wakili ya yanke jiki ya fadi a gidansa dake unguwar Gwarinpa a Abuja da safiyar yau an kuma garzaya da shi zuwa Asibitin View Point inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Fitar Wakili ta karshe ita ce daurin auren yar gidan Dangote da ya halarta a Kano jiya ranar Juma’a.

An gano cewa dan majalisar dattawan ya shirya zuwa Yola babban birnin jihar Adamawa a yau.

Wata majiyar ta ce ya kira direbansa domin ya dauke shi ya zuwa filin jirgin sama dake Abuja kafin ya fadi ya mutu.

Marigayin na daya  daga cikin sanatocin dake kan gaba wajen goyon bayan shugaban kasa Muhammad Buhari.

You may also like