Sanata Muhammad Ali Ndume Ya Tallafawa ‘Yan Gudun Hijira Dake Abuja Sanatan Mai wakiltan Kudancin Borno a Majalisar tarayya ya tallafawa yan gudun hijira yan Asalin kudancin Borno dake Abuja da Babura 50 da zummar taimako da kuma dogara da kai.

Ahannu guda Sanatan ya tallafa kungiyar Mata dana matasa da Naira 500000 ko wanen Su suma da zummar tsayawa da kafafunsu.

Daga karshe Wanda sukaci gajiyar, sunyi godiya da Sam barka dangane da wannan tallafi da Suka samu

You may also like