Sanata Sani Yariman Bakura Zai Tsaya Takarar Shugaban Najeriya A 2019Tsohon gwamnan Zamfara kuma Sanata a yanzu Ahmed Sani Yariman Bakura ya aiyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a 2019 in Allah ya kai mu.

Yariman Bakura ya ce ya shirya tsaf don takarar kamar yadda ya taba gwadawa a 2007 a tsohuwar jam’iyyar adawa ta ANPP. 

“Duk da haka sharadin takarar ta wa ya dogara ne ga idan shugaba Buhari ba zai yi takara ba, don in zai yi zan mara ma sa baya kamar yadda na yi a 2015”

Sanata Sani ya ce ya na da muradin in Allah ya hukunta ya zama shugaban Nijeriya zai yi yaki da yunwa a matsayin babban muradin gwamnatinsa.

You may also like