Sanata Shehu Sani Ya Nemi Buhari Da Yayi Ritaya Daga Ministan Mai Bisa Badakalar Da Aka SamuDan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan yi ajiye mukamin Babban Ministan mai bayan da karamin Ministar mai, Ibe Kachikwu ya rubuta masa wata wasika inda ya fallasa yadda Shugaban kamfanin mai na kasa ( NNPC), Baru ke yin gaban kansa wajen tafiyar da kamfanin.

Dan majalisar ya nemi Buhari da ya binciki zargin da karamin Ministan ya gabatar a kan shugaban kamfanin NNPC wanda a cewarsa, ta haka ne kadai Buhari zai tsira da mutuncinsa. Tuni dai, majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki Shugaban kamfanin na NNPC.

You may also like