Sanata Wakili ya nemi a kawo masa shayi kafin ya fadi kasa a mace


Wani mamba a majalisar wakilai ta tarayya, Muhammed Sani Abdu, a ranar Talata ya bayyana yadda Sanata Ali Wakili (Fagacin Bauchi) ya mutu.

A cewarsa,Wakili ya saka kaya ya shirya yin  tafiya Yola, jihar Adamawa domin halartar bikin yar gidan sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustafa.

Amma kafin ya bar gida, Sani Abdu wanda ya yi magana a zauren majalisar wakilai, ya ce marigayin ya nemi matarsa ta shirya masa abinci da zai ci kafin ya fita.

“Ta shirya masa fate inda ta kawo masa ya ci.Amma Wakili ya fada mata yana son abu marar nauyi kamar shayi.

“Ta koma ta kawo masa shayi kawai sai tazo ta tarar da mijinta ya fadi ƙasa.”

Sani Abdu ya tuna yadda ya yiwa marigayin wanka tare da  hada  gawar domin binnewa tun da an fada masa abin da ya faru.

You may also like