Sanata Zai Gyara Kurakuran Tarihin Sarauniyar Zazzau Ta Hanyar Fim


Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta daukar nauyin shirin fim da zai nuna hakikanin tarihin Sarauniya Amina ta Birnin Zazzau domi gyara dimbin kurakuran da Turawa suka yi a kan  tarihinta.

Kwamarade Sani ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai kabarin Abakwa, mahaifiyar Sarauniya Amina da ke garin Turunku, cikin Karamar Hukumar Igabin jihar Kaduna.

Shehu Sani ya ce, “Wannan ziyara da na kawo kabarin Abakwa, wadda take mahaifiya ga Sarauniya Amina ta Zazzau, na yi ne domin kara kusanta da abubuwan da suka faru a tarihi kusa da mu.”

Sanatan ya jaddada cewa Sarauniya Amina ta bayar da gudunmuwa matuka a ci gaban rayuwa, haka zalika ta koya mata yadda za su kwatar wa kansu ‘yanci ta fuskoki da dama, amma sam ba a yi rubutu a kai ba.

“Ina ganin wannan abu a matsayin babban kalubale gare mu. Na zo domin in ga me zan iya a kashin kaina wanda tarihi zai bayyana hakikanin Masarautar Amina, ta yadda yara masu tasowa za su amfana.”

“Ina amfani da wannan dama, don in sanar da ku cewa zan dauki nauyin fim wanda zai bayyana hakikanin tarihin Sarauniya Amina, kuma Jami’o’i daga Arewacin kasar nan su za su yi aikin binciken kwakkwafi kan tarihin nata. Da suka hada da Jami’ar ABU Zariya, Jami’ar Bayero Kano, da ta Usman Danfodiyo Sokoto, da wasu manyan kwalejojin ilmi daga sassan jihohi, ciki har da Neja.” In ji shi.

Sanatan ya kara jaddada cewa an bar wasu mutane daga waje sun murguda tarihin Amina, “saboda haka ya zama wajibi mu tashi tsaye wajen fada wa duniya hakikanin tarihin rayuwarta.”

Ya ce tarihin kasar nan ya samu tawaya daga wajen Turawan mulkin mallaka, domin labarun da aka rika bayarwa sun takaita ne daga shekarar 1914, watau lokacin da aka hada Arewaci da Kudanci.

Haka zalika, ya ce akwai abubuwa da yawa wadanda Turawa suka kwashe da suka shafi tarihin Abakwa, saboda haka zai kai maganar Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, kuma zai tabbatar da ganin an dawo da su.

“Muna da masaniyar irin fadi-tashin da iyaye da kakanninmu suka yi wajen ganin sun kare martabarmu; kuma su tabbatar mun zamo al’ummar da duniya za ta yi alfahari da ita.

“Ina da yakini idan za mu mayar da hankali kan gadon da aka bar mana, za mu kara kima da daraja a idon duniya.” In ji Shehu Sani.

You may also like