Sanatoci Da Masu Zanga Zanga Sun Raka Dino Melaye Kotu


A yanzu haka dandazon magoya bayan Sanata Dino Melaye, ciki kuwa har da Sanatoci da dama sun yi cincirindo a kotun da ake shari’ar sa a Abuja.

Ana tuhumar Dino Melaye ne kan bayar da bayanan karya inda ya kantara kazafin cewa an yi nemi halaka shi ta hanyar wani hari da aka kai masa har gida.

Magoya bayan na Dino, su na dauke da kwalaye da faska-faskan fastoci masu dauke da hotunan sa, kuma an rubuta: “Mu na bayan Dino Melaye” da manyan rubutu a jikin kowace babbar fasta.

Cikin sanatocin da suka raka shi kotu, har da Sanata Ben- Murray Bruce daga jihar Bayelsa.

You may also like