Sanatoci sun bayar da kyautar buhunan shinkafa sama da 1000 ga ma’aikatan jihar Kogi


Wasu sanatoci  sun bayar da taimakon shinkafa ga ma’aikatan jihar Kogi wadanda ba abiya su albashi ba na tsawon watanni 11.

Dino Melaye Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya bayyana haka bayan zaman majalisar na ranar Laraba ya ce kyautar an yi ta ne domin ragewa ma’aikatan wahalar da suke ciki.

Tun da fari sanatan ya jawo hankalin abokan aikinsa kan halin da ma’aikatan jihar ta sa ke ciki.

Inda ya yi kira ga sauran yan Najeriya masu hannu da shuni da su taima kawa ma’aikatan.

Melaye ya bayyana sunan mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu a matsayin wanda ya fi bada kyauta mafi tsoka.

You may also like