Sanatocin Najeriya za su tallafa wa ‘yan gudun hijira


 

 

Mambobin majalisar dattawan Najeriya sun amince da bai wa ‘yan gudun hijirar kasar tallafin kudade, in da kowanne mutum guda daga cikinsu zai bayar da Naira dubu 300.

Wannan dai wani mataki ne na kokarin rage wa ‘yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanoni daban-daban a duk fadin kasar radadin da suke fama da shi.

Sanatocin sun cimma matsayar tara kudin ne bayan sun tafka maharawa kan tashe- tashen hankulan da ke ritsa wa da jama’a a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, in da rikicin Boko Haram ya fi kamari.

Majalisar dattawan dai na da mambobi guda 109, abin da ke nufin cewa, za su tara kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 32 da dubu 700.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like