Masana’antar dinka Suturar Musulunci na ci gaba da habbaka a kasar Turkiyya wadda kusan illahirin ‘yan kasarta Musulmai ne.
Wannan kasuwancin dai ya yi daidai da al’adun kasar da kuma manufar jam’iyyar AKP ta Recep Tayyip Erdoğan wadda ke kishin Musuluci.
Hukumar dinka Tufafi ta Dubai ta ce wannan kasuwancin na da albarka sosai domin a duk shekara za’a iya samun zunzurutun kudi dalar Amurka bilyan 500.
Da yake magana da wani dan jaridar Anadolu Agency,shugaban kamfanin dinka suturar Musulunci ta kasar Turkiyya Kerim Ture, ya ce a yanxu ‘yan mata Musulmai na da cikakkiyar ‘yanci a wajen zaben tufar da zasu saka ba tare sun yi shiga irin ta tsaffi ba.
Daya daga cikin mambobin kungiyar masu halin rikau ta Turkiyya Ozgur-Der wato malam Hulya Sekerci ya ce mun yi na’am da raya suturar Musulunci a kasar Turkiyya,domin abu ne matukar muhimmanci,amma ba mu yarda da bukukuwan nuna tufafi da wasu madinka ke yi,saboda ya yi hannun riga da al’adu da kuma addininmu.