Sarkin Kano Muhammad Sunusi II, ya nemi ƙungiyar fulani ta Miyetti Allah da ta tona asirin ɓatagarin fulani makiyaya dake cikinta.
Da yake magana a taron shugabannin ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a Minna, jihar Niger a ranar Lahadi Sunusi yace ba dukkanin fulani bane ɓata gari.
Sarkin ya ce ƴan Najeriya su daina kawo zancen ƙabila duk lokacin da aka aikata wani laifi.
“Ya kamata ƴan Najeriya su kaucewa alaƙanta wata ƙabila duk sanda aka aikata wani laifi, laifi bashi da tambarin wata ƙabila,” yace.
“Ya kamata Miyetti Allah ta haɗa kai da Gwamnonin Niger, Kogi, Nassarawa da kuma Kano wadanda suka nuna sha’awarsu ta bada filayen kiwo domin a samu inganatasu.”
Ana sa ɓangaren shugaban shiya na ƙungiyar, Gidado Siddiki ya ce maganin rikicin fulani da makiyaya shi ne tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar.
Ya yabawa hanyar da gwamna Willie Obiano na jihar Anambra da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu suka bi wajen maganin rikicin fulani da manoma.