Saraki Da Dogara Sun Bukaci Buhari Da Ya Ja Kunnen Shugaban Ƴan Sanda


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun nemi Shugaba Buhari ya tilasta Shugaban Rundunar ‘yan sanda, Ibrahim Idris kan ya bayyana gaban majalisar don yin mata bayani kan yadda ‘yan sanda ke wulakanta, Sanata Dino Malaye.

Shugabannin majalisar sun gabatar da wannan bukata ce a yau a lokacin da suka sadu da Shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja inda suka yi Allah wadai da yadda aka kai Sanata Dino Malaye kotu a kan kujerar marasa lafiya wanda a cewarsu, babu inda ake yin haka a duk fadin duniya.

You may also like