Saraki Na Yunkurin Kare Harkar Noman Kaji Daga Durkushewa


​Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, yace majalisar dattawa zata taimaka ta hanyar yin dokoki, da kuma kawo wasu tsare-tsare da zasu kare masu noman kaji daga kalubalen da suke fuskanta na masu fasa kwaurin kaji zuwa cikin kasarnan. 

Saraki na wannan maganar a jihar kwara, lokacin da yake kewaya wa wurin da aka tsugunar da manoman da aka kora daga Zimbabwe a arewacin jihar, inda suke gudanar da noma a manyan gonakin da aka tsugunar da su. 

Yace karfafa fannin kiwon kaji,zai sa manoman su bada gudumawar su a kokarin da kasarnan take na dogaro da kai a fannin samar da abinci 

Saraki ya samu rakiyar,Gwamnan babban bankin kasa wato CBN, da Shugaban kwamitin harkokin noma na majalisar,Sanata Abdullahi Adamu, da Gwamnan jihar  Abdulfata Ahmad, da kuma Sanata mai wakiltar arewacin jihar Alhaji Shaba Lafiagi.

Yace babu wani dalili da zai sa ace manoman kajin Najeriya, baza su iya samar da kaji ba ga daukacin yankin Afirika ta yamma ba. 

You may also like