Saraki Ne Ya Nemi Na Kawo Ƙudirin Tsige Buhari A Majalisa – Sanata Matthew Urhoghide


“Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne ya ce min na kawo kudirin tsige shugaba Muhammadu Buhari a zauren majalisa, saboda hakan ya taimaka wajen samuwar kariya ga mu sanatocin.

“Kun san dai yanzu haka EFCC na kan bincikar mataimakin shugaban Majalisar, sannan Sanata daga jihar Delta yanzu haka yana Kurkuku, ga kuma Sanata Dino yana fuskantar kiranye.

“Tabbas na yi mamakin yadda ‘yan uwana sanatoci suka juyawa kudirina baya a zauren majalisa, babban abun mamakin ma shine yadda Hatta Gwamnan jiha ta haushi na yake ji, saboda wannan kudiri da na yi a majalisa, hatta al’ummar da nake wakilta sun harzuka da ni, kuma sun fara shirye-shiryen dawo da ni gida sakamakon wancan aiki da na yi. Maganar gaskiya na yi nadama.

“Don Allah ku yafemun wallahi Shugaban Majalisa ne ya sanya ni, ba ra’ayi na bane, shi ya kamata ku ji haushi ba ni ba.

Ko kadan bana fatan yin rigima da shugaban kasa Muhammadu Buhari, saka ni aka yi, amma zan yi wa al’ummar Nijeriya bayani cikakke a gobe Litinin”, Inji Sanata Matthew Urhoghide.

You may also like