Saraki ya Ba Kwamitocin majalisar awowi 24 Su Kammala Aikin Kasafin Kudi


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ba kwamitocin majalisar awowi 24 kan su kammala aikin kasafin kudin 2019.

Saraki ya ce, kwamitoci 20 har yanzu ba su kammala aikinsu ba inda ya jaddada masu cewa bai kamata su gurgunta kokarin da majalisar ke yi na ganin da amince da kasafin wanda Shugaba Buhari ya gabatarwa majalisar tun a watanni shida da suka wuce.

You may also like