Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnatin Buhari za ta mayar da hankali wajen samarwa matasa aikin yi a maimakon zargin gwamnatocin da suka shude kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.
Ya kara da cewa babban abin da ke kara yawan rashin aiki a tsakanin matasa shi ne, yawan haihuwa wanda kuma ya zarce ci gaban tattalin arziki sannan kuma tsarin koyar a Makarantu bai tanadi koyar da sana’o’in dogaro da kai ba sai kuma durkushewar masana’antu.