Saraki Ya Yaba Wa Shugaba Buhari Bisa Nasarar Murkushe BokoHaram Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yaba wa Shugaban Kasa, Muhammad Buhari bisa nasarar da sojojin Nijeriya suka samu na murkushe sansanin ‘yan Boko Haram na karshe da ke cikin dajin Sambisa.
Saraki ya ce wannan nasara ta zo daidai da lokaci na karshen shekara inda ya bayyana nasarar a matsayin wata kyauta daga Ubangiji ga mutanen Nijeriya. Shugaban majalisar ya kuma yaba wa ‘yan Nijeriya bisa irin hadin kan da suka baiwa sojoji wajen kaiwa ga wannan nasara inda ya kalubalance su kan su ci gaba da bayar da goyon bayan wajen tona asirin ‘yan Boko Haram da suke cikin jama’a

You may also like