Saraki Ya Zubar Da Ƙimar Majalissar Dattawa – Ndume


Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ya yi matukar yin nadama wajen goyon bayan Sanata Bukola Saraki ya zama Shugaban majalisar Dattawa.

Sanata Ndume ya ce a halin yanzu majalisar ba ta da wata kima a idon ‘yan Nijeriya saboda salon shugabancin Saraki da kuma yadda wasu ‘yan lelansa ke gudanar da harkokinsu ta hanyar zubar da mutuncinsu.

Ya kara da cewa Saraki ya mayar da kansa Shugaban sanatoci a maimakon Shugaban majalisar Dattawa inda yake fifita kansa a kan sauran abokan aikinsa.

You may also like