Sarakunan gargajiya za su tabbatar da an sake zaɓen Buhari a 2019


Sarkin Maradun dake  Zamfara, Alhaji Garba Tambari ya ce wasu sarakunan gargajiya dake faɗin kasarnan sun yanke shawarar tabbatar da zaɓen shugaban kasa Muhammad Buhari, a shekarar 2019.

Tambari ya bayyana haka  lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ziyarar ta’aziyar da ya kaiwa shugaban ƙasa Muhammad Buhari ranar Lahadi a Daura.

A cewar sarkin dukkanin ƴan ƙasa wadanda kewa ƙasarnan fatan alheri dole su goyi bayan sake tsayawar shugaban ƙasa Muhammad Buhari takara a shekarar 2019 idan har ya yanke hukuncin zai tsaya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa shugaban kasa na ziyarar kwanaki biyar ta ƙashin kansa a Daura kuma har yanzu ya gaza fitowa fili ya bayyana matsayinsa kan batun ko zai sake tsayawa takara a shekarar 2019.

 Amma kuma sarkin ya dage kambakansa cewa ” dukkanin mai yiwa ƙasarnan fatan arziki, yake yi wa kasarnan fatan zama lafiya zai so mai girma shugaban ƙasa ya cigaba da mulki bayan shekarar 2019.Saboda haka muna fatan zai cigaba da izinin Allah.”

Tamabari wanda yace yaje Daura ne ziyarar goyon baya ga shugaban  ya kuma ya ba masa kan yadda yake hidimtawa ƙasarnan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like