Sarki Sunusi Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Da Ake Masa Na Ɓarnatar Da Kuɗaɗe


Emir-Kano-Sanusi-Lamido

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi yayi watsi da zargin da ake masa na ɓarnatar da kuɗi har naira biliyan 6  daga baitil malin masauratar ta kano.

Da yakewa manema labarai jawabi ta bakin Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali, wanda shine me kula da harkokin kuɗin masauratar, yace daga watan Yuli na shekara ta 2014 lokacin da aka naɗa sarkin Kano Muhammadu Sunusi zuwa yanzu masauratar ta kashe kuɗi naira biliyan biyu da miliyan ɗari tara(2,900,000,000) ne kawai, ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suke yaɗawa ba.

Wali ya bada ƙididdigar kuɗin inda yace marigayi Sarkin Kano Ado Bayero yabar kuɗi kimanin naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari tara (1,900,000,000), ba kamar yadda ake yaɗawa ba cewa sarkin yabar kuɗi har Naira biliyan huɗu(4,000,000,000).

You may also like