Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Farouk Umar ya roki Shugaba Muhammad Buhari kan ya sake duba batun kudirin kafa rundunar Peace Corps” wanda ya ki amincewa da kudirin bayan majalisar tarayya gabatarwa Shugaban da shi a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Sarkin ya yi wannan rokon ne a lokacin da Kwamandan rundunar ta kasa, Dakta Dickson Akoh ya ziyarce shi a fadarsa da ke Daura inda Sarkin ya nuna cewa amincewa da kafa rundunar zai samar da guraben aiki ga matasa ba ya ga inganta harkokin tsaro a Nijeriya.
A nan, Dan Majalisar Dattawa Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ne a lokacin da yake raba kananan rediyo don Jin Labarai ga dattawan mazabarsa.