Sarkin Dayafi kowanne Sarki Dadewa A karagar Mulki ya Rasu. 


Sarkin kasar Thailand, Bhumibol Adulyadej, wanda shi ne sarkin da ya fi kowanne dadewa a kan sarauta, ya mutu bayan ya kwashe shekara 70 akan gadon sarauta.
‘Yan kasar Thailand na matukar so tare da girmama Sarkin, mai shekara 88.
Ana ganin sa a matsayin wani mutum da ke fada-a-ji a kasar da ke fama da tashin-tashina da juyin mulki da dama.
A ‘yan shekarun bayan nan ne ya sha fama da rashin lafiya lamarin da ya sa ba ya fitowa sosai cikin jama’a. 
Mutuwar Sarkin dai ta zo ne a lokacin da Thailand ke karkashin mulkin soja bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2014.
A ranar Lahadi ne dai masarautar ta yi gargadin cewar rashin lafiyar Sarkin ta tsananta


Like it? Share with your friends!

0

You may also like