Sarkin Kano ya yi kira da a rika yiwa gwamnoni, yan siyasa, sarakuna gwajin shan miyagun kwayoyi 


Sarkin Kano,Malam Muhammad Sunusi II yayi kira da a samar da wata doka da zata tilastawa yan siyasa, sarakuna, da sauran masu rike da ofisoshin gwamnati zuwa asibiti domin ayi musu gwajin shan miyagun kwayoyi.

Sanusi wanda yayi wannan kira a wurin bude wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da majalisar dattawa ta shirya kan ta’ammali da kwayoyin magani ba bisa ka’ida ba a Najeriya inda ya ce zai yi farin ciki yaga ya mika kansa domin ayi masa gwaji ko yana ta’ammali da miyagun kwayoyi.

” Idan muka fara kafa irin wannan misali, matasa masu tasowa za su fahimci cewa inda suka shiga shan miyagun kwayoyi to kuwa za su takaita damar da suke da ita ta zama shugabanni.

“Yan’sanda, sojoji da sauran masu kayan sarki bai dace ace sun kasance masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ba.

 Sarkin ya koka cewa kasarnan na fuskantar wata babbar musifa inda ya lura cewa ya waitar shan miyagun kwayoyi wata manuniya ce dake nuna gazawar gwamnonin mu.
Ya bada shawarar cewa yaƙi da shan miyagun kwayoyi ya kamata ya zamo kan gaba a cikin jerin manufofin gwamnati.

You may also like