Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi na II zai bi Sahun Shugaban kasa Muhammad Buhari wajen aurar da ‘yar sa, Fulani Saddika Sanusi.
Rahotanni na nuna cewa sarkin zai bayar da ‘yar ta sa ne ga Malam Abubakar Umar Kurfi a ranar Juma’a, 23 ga watan Disamba a fadarsa da ke cikin birnin Kano.
Tuni an yi kamun auren a ranar 18 ga watan nan, inda aka nuna tsantsar gargajiyar bahaushe.
Ga wasu daga cikin hotunan kamun kamar wanda Maigaskiya ya dauka