Sarkin Katagum ya rasu yana da shekaru 89


Allah ya yi wa Sarkin Katagum, Alhaji Muhammad Kabir Umar, rasuwa.Ya mutu da yammacin ranar Asabar 9 ga watan Disamba a Azare.

Sarkin wanda ya kasance ministan ilimi na yankin arewa a  zamanin sardauna.

Marigayin ya rasu yana da shekara 89 a duniya kuma yabar ya’ya 49 cikinsu akwai Mustapha Muhammad wazirin Katagum.

Gwamnan jihar Bauchi  Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana jimaminsa kan mutuwar sarkin wanda ya bayyana a matsayin mutum mai gaskiya da kuma riko da koyarwar annabin tsira Muhammad (SAW).

Shima kakakin majalisar wakilai ta kasa Yakubu Dogara ya bayyana mutuwar sarkin a matsayin wani babban rashi ga dukkanin al’ummar Najeriya ba al’ummar Bauchi kaɗai ba.

You may also like