Sarkin kasar Morocco Muhammad na 6 ya kori wasu daga cikin ministocin gwamnatin rikon kwarya ta kasar.
Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya ne sarkin ya sanya hannu kan takardar tsige ministocin guda 12, wadanda dukkaninsu suna daga cikin ‘yan majalisar dokokin da suka lashe zabe da aka gudanar a kasar a ranar 7 ga wannan wata na Oktoba.
Bisa ga dokokin kundin tsarin mu8lkin Morocco, mutum daya ba ya rike mukamin minista alhali yana a matsayin dan majalisa.
Bayan gudanar da zaben na Morocco majalisar ministocin ta yi murabus, amma sarkin ya sake nada domin ci gaba da gudanar da ayyuka na wucin gadi.