Sarkin Musulmi Mai Murabus Ibrahim Dasuki Ya Rasu


Labarin da ke ishemu shi ne na rasuwar tsohon Sarkin Musulmi mai murabus, Alhaji Ibrahim Dasuki.

Alhaji Ibrahim Dasuki dai shi ne Sarkin Musulmi na 18 a tsarin halifancin Shehu Usmanu Dan Fodiyo, kuma an nada Dasuki a matsayin Sarkin Musulmi a shekarar 1988 a karkashin jagoranci shugaban kasa na wancan lokaci Ibrahim Badamasi Babangida,

Marigayi Dasuki ya samu shekaru 8 a matsayinsa na Sarkin Musulmi, inda a shekarar 1996 gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Sani Abacha ta tsige shi daga wannan matsayi na Sarkin Musulmi tare da tsare shi bisa wasu zarge-zarge

Kafin Marigayi Dasuki ya zama Sarkin Musulmi a shekarar 1988 shi ne Baraden Sokoto

Marigayi Dasuki na daya daga cikin manyan mutanen Marigayi Ahmadu  Bello Sardaunan Sokoto kuma amini ne ga Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Marigayi Dasuki dai shi ne mahaifin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki da ke fuskantar tuhuma daga wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari

An haifi marigayi Ibrahim Dasuki a ranar 31 ga watan Disamba, 1923 kuma ya rasu a jiya Litinin 14 ga watan Nuwamba, 2016 yana da shekaru 93

Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu a Abuja

Da fatan Allah ya yafe kura-kuransa, ya yi masa rahama, amin

You may also like