Sarkin Musulmi ya bukaci karfafa auratayya tsakanin mabiya addinai


Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar

 

Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar ya bada shawarar karfafa alakar auratayya tsakanin mabiya Addinin Musulunci da kuma Kirista, domin karfafa hadin kai da zaman lafiya tsakanin mabiya addinan guda biyu.

Sarkin Musulmin ya yi kiran ne a wajen wani taro da kungiyar Kiristoci matasa ta shirya a babban birnin tarayyar Najeriya.

Wani Masanin addini kuma mai sharhi kan al-amuran yau da kulum, Mallam Tahir Hassan Bagega ya ce addinin musulunci bai hana auratayya tsakanin Musulmi da Kirista ba, sai dai kuma a dokar Addnin bai hallata mace musulma ta auri namiji kirista ba.

Mallam Bagega ya ce kamata yayi a maida hankali kan tabbatar da adalci ga kowa, kasancwar koda an karfafa auratayyar masu banbancin addini in har babu adalci ba lallai bane a samu tabbataccen zaman lafiya.

You may also like