Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya roki gwamnatin tarayya kan ta sassauta dokar hana shigo da shinkafa da Motoci ta iyakokin Najeriya inda yace matakin ya kara jefa al’umma kasa cikin kunci.
Ya ce akwai yiwuwar wannan haramci kan iya harzuka al’ummar Najeriya wadanda a halin yanzu ke cikin mawuyacin yanayi, ya kuma bayar da tabbacin cewa masarautar za ta ci gaba da bayar da hadin kai ga manufofin gwamnati.