Sarkin Musulmi Ya Wanke Fulani Daga Zargin Kai Harin Binuwai


Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Saad Abubakar ya jaddada cewa ba Fulani makiyaya suka kai harin Binuwai ba inda ya yi Allah wadai kan kiraye kirayen haramta kungiyoyin makiyaya.


Sarkin Musulmin ya ce tun yana karami yasan makiyaya da wannan sana’a ta kiwo kuma an kafa kungiyar Miyetti Allah ne tun a shekaru 36 kuma maganar haramta kungiyar tamkar kira ne ga haramta kungiyoyin Yarbawa ta Afenefere da na Igbo ta Ohanaeze. Sarkin ya kara da cewa a kowace kungiya ba a rasa samun bara- gurbi.

You may also like