Sarkin musulmi zai jagoranci addu’o’i na musamman ga Buhari da rikicin Kudancin Kaduna


Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad zai jagoranci addu’o’i na musamman domin nema wa shugaban kasa Muhammadu Buhari Karin lafiya da kuma samun zaman lafiya mai dorewa a kudancin jihar Kaduna.
A cewar jaridar Premium Times, Sakataren kungiyar Jama’atu Dr. Khalid yace za’a gudanar da zaman addu’o’in ranar Lahadi mai zuwa a garin Kaduna.

Yace gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, Sarkin Zazzau, Shehu Idris, Sarkin Musulmi, Dr, Abubakar Sa’ad da Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna duk za su halarci zaman addu’o’in.

Bayan haka sarkin musulmi yace masallatan Juma’a a jihar su gudanar da irin wadannan addu’o’i a masallatansu ranar juma’a.

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya jagoranci malamai da limaman jihar domin gudanar da addu’a ta musamman na neman Allah ya karawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya.

Bayan haka kuma an yi irin hakan a garin Bauchi inda gwamnan jihar Mohammed Abubakar da sarkin Bauchi Rilwanu Adamu suka jagoranci addu’o’in.

A lokacin gudanar da wannan addu’o’i sarkin Bauchi yayi kira ga masarautun dake kasar Bauchi duka da su gudanar da irin wadannan addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like