Sau nawa aka kara tsakanin Real da Man City a Champions?Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid da Manchester City za su fafata a wasan daf da karshe a Champions League na kakar nan.

Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi waje da Chelsea da cin 4-0 gida da waje, tun kan nan ita ce ta fitar da Liverpool.

City kuwa ta yi nasarar doke Bayern Munich da cin 4-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 ranar Laraba a Jamus a wasa na biyu a quarter finals.

Hakan ne ya sa Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla za ta kece raini da City, wadda ba ta taba lashe kofin ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like