Saudi Arabia : An kama wasu Alhazan Najeriya da Hodar Ibilis


A yau laraba ne Hukumomin saudiyya suka tabbatar da kama wasu mutum 3 daga Alhazan Najeriya da wani abu da ake zaton Hodar ibilis ce wato Cocaine a turance. 
An kama alhazan ne a birnin madinah inda aka aka tabbatar da alhazan ‘yan asalin kasar Najeriya, a yanzu haka dai suna nan a kulle a hannun Hukumomin saudiyya.

Alhazan dai suna cikin alhazai 505 da kasar Najeriya ta fara kaiwa kasar saudiyya.

You may also like