Saudiyya da Iran: Bude ofishin jakadanci | Labarai | DWMinistan harkokin kasashen waje na Iran din Hossein Amirabdollahianya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya ngudanar a birnin Berut fadar gwamnatin Lebanon, yayin ziyarar aiki da yake a yanzu haka a kasar. Sai dai kuma, Amirabdollahian bai bayar da takamaimiyar ranar da kasashen biyu za su yi bikin sake bude ofisoshin jakadancin nasu ba. A baya dai Tehran da Riyadh na yi wa juna kallon hadarin kaji, kafin a watan Marsi din da ya gabata su amince da farfado da dangantakar da ke tsakaninsu.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like