Saudiyya ta ci alwashin mallakar makamin nukiliya matukar kasar Iran ta mallaka


Hakkin mallakar hoto:Daily Trust

Kasar Saudiya ta yi gargadin cewa za ta mallaki nata makamin kare dangi matukar abokiyar hamayyarta a yankin wato kasar Iran ta mallaka.

Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman ya fadawa gidan Talabijin na  CBS dake kasar Amurka cewa kasarsa bata so ta mallaki makamin kare dangi.

“Amma babu tantama idan Iran ta kirkiri bom na nukiliya, to zamu bi sawunta da gaggawa,” ya ce.

Kasar Iran ta dakatar da shirinta na mallakar makamin nukiliya tun a shekarar 2015 bayan wata yarjejeniya da ta cimma da manyan kasashen duniya sai dai a yan kwanakin nan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar janye kasarsa daga yarjejeniyar.

Yarima Muhammad Bin Salman wanda shine  mai jiran gadon sarautar mulkin kasar, kuma ministan tsaro ya yi wannan magana da kafar yada labarai ta CBS a wani shirinsu na tsawon awa guda.

You may also like