Saudiyya ta ciyo bashin dalar Amurka bilyan 17.5


 

Kasar Saudiyya wadda ke fuskantar matsalolin tattalin arziki,ta ciyo bashin dalar Amurka bilyan 17.5 daga hannun masu zuba jari n kasashen waje.

Bankin HSBC ce ta rawaito wannan labarin a ranar alhamis din nan da ta gabata.

Wannan shi ne karo farko da kasar Saudiyya ta taba cin bashi tun a lokacin da aka kafa masarautar.

Saudiyyar wacce ita ce ta farko a jerin kasashen da suka fi arzikin man fetur a duniya, na ci gaba da fama da kariyar tattalin arziki wanda ya samo asali daga faduwar farashin man fetur.

Raguwar da kasafin kudin kasar ya yi a bana da kusan dalar Amurka bilyan 87,yasa shugabannin Saudiyya daukar matakan tsuke bakin aljuhu da kuma ciyo bashi daga masu hannu da shunin kasashen waje.

You may also like