
Asalin hoton, Reuters
Iran ta ce Saduiyya ta gayyaci shugaban ƙasar Ebrahim Raisi domin zuwa wata ziyara a ƙasar – mako ɗaya tun bayan da ƙasashen biyu suka amince su ci gaba da hulɗar diflomasiyya.
An bayyana cewa batun gayyatar na kunshe ne cikin wata wasika da Sarki Salman ya rubuta, sai dai ƴan ƙasar basu tabbatar da hakan ba.
Ƙasashen biyu da ke yankin gabas ta tsakiya, sun yi ta samun takun-tsaka na tsawon shekaru.
China tana cikin ƙasashen da suka shiga tsakani wajen ganin ƙasashen sun dawo ɗasawa, abu kuma da aka bayyana cewa zai sauya siyasar yankin.
Wani babban jami’in gwamnatin Iran, Mohammad Jamshidi, ya wallafa a shafinsa a tuwita kan batun ziyarar zuwa Saudiyya, inda ya ce mista Raisi ya yi maraba da batun da kuma nanata cewa Iran na da zummar faɗaɗa dangantaka.
Shi ma, ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya faɗa wa manema labarai cewa ƙasashen biyu sun amince su yi zama a matakin ministocin harkokin waje, inda ya ce an tsara gudanar da zaman ne a wurare guda uku.
Sai dai bai bayyana sunayen wuraren ba, ko kuma sanar da ranar da za a yi zaman ba.
Editan BBC na yankin Gabas Ta Tsakiya, Sebastian Usher, ta ce ci gaba da aka samu a dangantaka tsakanin ƙasashen biyu a baya-bayan nan wanda China ta shiga tsakani, na ƙara kyautata al’amura.
Ƙasashen sun sanar da cewa za su sake buɗe ofisoshin jakadancinsu nan da wata biyu da sake karfafa hulɗar kasuwanci da kuma na tsaro.
Ƙasashe da dama sun yi na’am da wannan ci gaba da aka samu, ciki har da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya, bayan yunkurin sulhunta ƙasashen a baya ya citura.
Saudiyya na yanke dangantaka da Iran ne a 2016 bayan da masu zanga-zanga suka afka wa ofishin jakadancinta a Tehran.