
Asalin hoton, CARLOS CLARIVAN/SCIENCE PHOTO LIBRARY
Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa za ta aika mace ta farko cikin ‘yan sama jannatin da za ta tura zuwa sararin samaniya a cikin wannan shekarar.
Matar mai suna Rayyanah Barnawi da namiji mai suna Ali Al-Qarni su ne mutane biyu da ƙasar za ta tura zuwa tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa cikin rubu’i na biyu na shekarar 2023.
Ƙasar ta ce manufar shirin ita ce ƙara yawa tare da ƙwarewar ‘yan sama jannati da ƙasar ke da su, da kuma cin moriyar ayyukan da harkar sararin samaniya ke tattare da su.
Haka kuma ta ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa binciken kimiyya da fasaha a ɓangarori da dama kama daga lafiya, da ci gaba zuwa binciken sararin samaniya.
‘Yan sama jannatin biyu Barnawi da Al-Qarni za su kasance cikin ma’aikatan kumbon AX-2 da za a harba.
Za a harba kumbon ne daga Amurka zuwa tashar sararin samaniyar ta ƙasa da ƙasa. Haka kuma shirin ya ƙunshi horar da ƙarin wasu ‘yan sama jannatin biyu Mariam Fardous da Ali Al-Ghamdi.
Shugaban hukumar gudanarwar sararin samaniyar Saudiyya Engr. Abdullah Al-Swaha ya ce a shirye jagororin ƙasar suke wajen tallafa wa shirin samar da tashar sararin samaniyar.
Asalin hoton, SPACEX
Ta hanyar wannan shirin, ƙasar Saudiyya za ta fara binciken kimiyya a matakan kimiyyar sararin samaniya da bunƙasa karfinta ta yanda za ta gudanar da bincikenta da kankin kanta kan kyakkyawar makomar ƙasar.
Sannan hakan zai ƙara wa ɗaliban jami’a sha’awar karantar fannin Kimiyya da fasaha da injiyanci, da lissafi, tare da samar da yawan mutane da ƙwarewa a wannan fannin.
Haka kuma, Mohammed Al-Tamimi, babban shugaban hukumar sararin samaniyar Saudiyya, ya bayyana farin cikinsa ga jagororin ƙasar saboda tallafa wa hukumar domin ƙara bunƙasa hukumar.
Wanda hakan ya taimaka wajen rage matsaloli da yawan ƙalubalen da hukumar ke fuskanta, lamarin da kuma zai taimaka wajen bunƙasa fannin sararin samaniyar ƙasar.
Harkar zuwa sararin samaniya alama ce da ke nuna irin ƙarfi da bunƙasar ƙasa a idanun duniya.
Haka kuma lamari ne da ƙasashen duniya ke gasa a kansa a fannonin Fasaha da injiniyanci da bincike da kuma ƙirƙire-ƙirƙire.
Wannan shiri ne da tarihi ba zai manta da shi ba, saboda zai sanya ƙasar zama ɗaya daga cikin ƙasashe ƙalilan na duniya da za ta aika ‘yan sama jannati biyu ‘yan ƙasa ɗaya a cikin kumbo ɗaya zuwa tashar sararin samaniya ta duniya kuma a lokaci guda.
Hukumar sararin samaniyar ƙasar ta kuma ce wannan shirin na haɗin gwiwwa ne da wasu ma’aikatun ƙasar ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar Tsaron ƙasar da ma’aikatar kula da wasanni da hukumar zirga-zirgar jiragen sama da hukumar asibitin ‘King Faisal Specialist Hospita’, da kuma cibiyar bincike ta ƙasar.
Sannan da haɗin gwiwwar wasu hukumomi na duniya da suka haɗa da ‘Axiom Space’ wadda ta ƙware a fannin sararin samaniya tare da ƙera kayayyakin da ake zuwa sararin samaniya da su a Amurka.
A baya dai an ji labarin cewa hukumar kula da sararin samaniyar Saudiyya ta ƙaddamar da shirin tura ‘yan sama jannatin.
Amma wannan shiri na aika ‘yan sama jannatin shi ne gagarumin aiki da hukumar ta cimma da nufin horar da ‘yan ƙasar domin zuwa tashar sararin samaniya.
Da nufin yin bincike na kimiyya da kuma shiga binciken ƙasa da ƙasa, da kuma makomar ayyukan da ke da alaƙa da sararin samaniyar ƙasar, abinda kuma zai taimaka wajen cimma muradun ƙasar nan da shekarar 2030.