Saudiyya zata dauki nauyin jinyar yaran Siriya 150


 

 

Saudiyya ta yanke shawarar tallafa wa wasu yaran yakin Aleppon kasar Siriya da ake ci gaba da jinya a wasu asibitocin da ke kan iyakar Turkiyya da Sham.

Wannan labarin ya fito ne daga bakin wani wakilin dindin na Saudiyya da ke a majalisar dinkin duniya,inda daga bisani kafar yada labarai ta SPA ta wallafa batun a zahirance,a ranar Alhamis din da ta shige.

Saudiyyawa dai,sun dauki alkawarin daukar nauyin jinyar wadannan yaran, ta hanyar kai wadanda ke cikin mayuwacin hali zuwa kasarsu da kuma sayen dukkanin na’urorin da suka dace a wajen kula da lafiyarsu.

Ga dai cikakken sanarwar da kafar watsa labarai ta Saudiyyar ta fitar : “Saudiyya zata amsa kiran kasashen Amurka da Sham, dangane batun taimaka wa yaran ‘yan uwanmu da ke a garin Aleppon kasar Siriya,wadanda kuma ake ci gaba da kai wa hare-haren bama-bamai mafi muni a duniya.Kasarmu ta yanke shawarar kawo sauki a cikin rayuwar ‘yan uwanmu Siriyawa,yin Allah wadai da halin gwamnatin Bashar Al Asad,jan hankalin kasashen duniya domin a dakatar da zubar da jinin ma’asumai,kafa mulkin da ya yi daidai da ra’ayin Siriyawa, domin ba su damar samun cikakken ‘yanci.Saboda hakan ya yi daidai da yarjejeniyar Geneva da kuma dokokin kasa da kasa”.

Tun bayan watsi da tsagaita wuta da gwamnatin Al Asad ta yi a ranar 19 ga watan Satumban da ta gabata ce,jiragen saman kasar Siriya da na Rasha suka fara luguden wuta a Aleppo da nufin farautar ‘yan adawa.Abinda ya haifar da mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama,musamman ma a unguwannin yammacin garin,inda sama mutane dubu 300 ke fama da matsalar rashin abinci da na magunguna.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like