Saukar Da Manhaja “App” A Waya Na Bukatar Karatun ‘Yanci!


 

 

Zamani na zuwa kuma ya wuce, a lokkuta da yawa mutane kan dauki wasu abubuwa a rayuwa cikin sauki. Karni na ashirin da daya 21, na dauke da wasu abubuwa da ya kamata musamman matasa su maida hankali akai. Bincike ya nuna da yawa mutane na amfani da wayoyin hannu batare da lura da yadda suke amfani dasu ta yadda ya kamata ba.

Mutane kan bayyanar da kansu ga duniya cikin rashin sani, wanda daga bisani hakan yana iya gabatar da wasu bayanan sirrin nasu ga duniya. Hakan na nuni da cewar mutane basu da wani sirrin kansu balle na wasu abubuwa da suke yi.

Hakan kan iya zama hadari ga rayuwar su da iyalan su. Sakamakon binciken ya nuna cewar mutane da dama kan saukar da manhajoji “App” a wayoyin su da basu duba tsari da ka’idojin amfani da manhajar ba, wanda wasu daga cikin manhajojin na dauke da damar nuna bayanan sirrin mutun, tahaka kowa zai iya gani, amma idan mutun ya kokarta wajen duba tsarin “Setting” zaiga abubuwan da suka kunsa a cikin manhajar.

Yana da matukar muhimanci mutane su dinga kulle kofar shiga yanar gizon wayoyi “Data” a dai-dai lokacin da basa amfani da ita. Domin tahaka wasu na iya satar bayanan su, da sirrikan su. Kana duk wata manhaja “App” da mutun zai saukar a wayar shi, to ya tabbata ya duba tsarin da ka’idojin manhajar kamin saukar da ita a wayoyin su, wanda idan mutun bai duba ba don gani ba, to a takaice ya bada ‘yancin shi da duk wani abu da zai sami wayar tashi.

You may also like