
Asalin hoton, Getty Images
Kimanin Amurkawa miliyan 200 ne zuwa yanzu aka ba su shawarar cewa su yi taka-tsantsan game da yanayin sanyi da ke ƙara tsananta gabanin hutun ƙarshen mako.
Fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka tsunduma cikin duhun rashin hasken lantarki, sannan an soke tashin dubban jiragen sama ranar Juma’a.
Aƙalla mutum 12 aka tabbatar sun mutu sanadin matsanancin sanyin a sassan ƙasar.
A Kanada ma, biranen Ontario da Quebec na fama da muku-mukun sanyin ƙanƙara da ya janyo katsewar wutar lantarki ga dubban gidaje.
A Amurka, farin hadari ya mamaye sassan da ya kai nisan kilomita 3,200 daga Texas zuwa Maine, sannan hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta ce wannan shi ne yanayin sanyi mafi tsanani da aka taɓa gani.
An yi hasashen zubar dusar ƙanƙara a Pennsylvania da Michigan. A Buffalo cikin jihar New York kuwa, ana tsammanin za a ga zubar dusar ƙanƙara da za ta iya kai wa har cinyar mutum wato kimanin inci 35.
Asalin hoton, Reuters
Hatta jihohin da sanyi bai cika tsanani ba a yankin Kudancin Amurka kamar Louisiana da Alabama da Florida da Georgia, an yi irin wannan gargaɗi na samun matsanancin sanyi.
Mace-macen da aka samu masu nasaba da muku-mukun sanyin sun haɗar da hatsarin motoci har da wani cunkoson motoci a Ohio, da ya janyo mutuwar mutum ɗaya.
Sama da jiragen sama 8,000 aka dakatar da tashinsu ranar Juma’a, kamar yadda shafin FlightAware ya ruwaito.
Lamarin kuma ya janyo cikas ga mutanen da ke son koma wa gidajensu don yin bukukuwan kirsimeti a cikin dangi.
Alƙaluma na baya-bayan nan na yawan mutanen da suka auka cikin duhu sanadin katsewar lantarki a sassan Amurka zuwa yammacin ranar Juma’a ya kai miliyan 1 da dubu 200, a cewar PowerOutage.us.
A Dakota ta Kudu, ƴan asalin Amurka, a cewar rahotanni, suna ƙona tufafinsu don jin ɗumi bayan da man fetur ya ƙare, ga shi kuma dusar ƙanƙara ta hana su fita.
Anna Halverson, wadda ke wakiltar Gundumar Pass Creek a sansanin Pine Ridge Reservation, ta faɗa wa jaridar Darsha Dodge cewa “muna cikin tsananin buƙatar agaji a nan.”
Asalin hoton, ANNA HALVERSON
“Muna da dusar ƙanƙara da ta kai tsayin wasu gidaje da ke da tsawon yadi 60 zuwa 70 a lokaci guda.”
Ta ce akwai wani iyali da madarar jariransu ta ƙare kuma sun shafe kwana huɗu suna cikin gida kafin su samu su fice saboda jaririnsu ya rasa abinci.
Mazauna yankin a yanzu sun koma ɗaukar matakan samun mafita ido rufe saboda rashin itacen wuta sanadin yanayin da ake ciki.
“Na ga yadda wasu a nan sansanin suke ƙona tufafinsu saboda ba za su iya samun itace ba,” in ji Ms Halverson.
Gwamnar South Dakota Kristi Noem ta buƙaci jami’an tsaro a jihar su yi jigilar itacen wuta daga wani daji na ƙasa da ke kusa zuwa ga ƙabilun Rosebud Sioux da Oglala Sioux.