An Sauke Su A Jirgi Don Sun Ambaci Sunan Allah


 

 

An fitar da wani Musulmi tare da matarsa daga jirgin sama bayan da wani ma’aikacin jirgin ya yi zargin cewa ya ga suna ta zufa suna ambatar sunan Allah (SWT), kamar yadda rahoton BBC ya bayar.

Faisal Ali tare da matarsa Nazia Ali sun kwashe tsawon mintuna 45 suna zaune a cikin jirgin sama na ‘Delta Air Lines’ lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Cincinnati, a jihar Ohio ta Amurka kafin daga bisani wani ma’aikacin jirgin ya umurce su da su sauko, za a yi musu tambayoyi.

Nazia Ali ta shaida wa manema labarai cewa, “Da muka nemi jin ko ana bukatar mu kwashe kayayyakinmu ne daga cikin jirgin, sai ma’aikacin jirgin ya ce kwarai kuwa, saboda ba za ku dawo cikin jirgin ba.”

Bayan an sauke su daga jirgin sun ga wani jami’an ‘yan sanda a bakin kofa yana jiransu. Ta ce, “Na firgita kwarai da na ga wani mutum yana daukar hotunan Faspo dinmu da wayar salularsa.”

Bayan an yi musu tambayoyi kan dalilin zuwan su Paris, dan sandan ya ce bai da wata tambaya da zai kara yi wa iyalan wadanda suka je birnin domin shakatawa don murnar cikarsu shekaru 10 a matsayin mata da miji.

Daga bisani sun ce wani ma’aikacin jirgin ya shaida musu cewa matukin jirgin ne ya bukaci a sauke su, saboda daya daga cikin ma’aikatan jirgin ya ce hankalinsa bai kwanta ba saboda ya ce ya ga Faisal yana boye wayar salularsa lokacin da ya zo wucewa, kuma yana ta zufa yana ambatar kalmar ‘Allah.’

Shi dai Faisal Ali ya ce yana turawa mahaifiyar sako ne da wayar salularsa don shaida mata cewa suna cikin jirgi lafiya kuma ta shirya tarbarsu a filin jirgin sama na Cincinnati.

Ya kara da cewa mai yiwuwa rashin wadataccen iska a cikin jirgin ne ya sa ya yi ta zufa saboda sun shafe kusan mintuna 45 suna zaune a cikin jirgin.

Kamfanin jirgin dai ya ba wadannan iyalai wadanda ke da ‘ya’ya uku masauki, inda suka kwana daya, yayin da wasu ma’aikatan hukumar hana fasakwauri suka kara yi musu tambayoyi kafin daga bisani aka sa su cikin jirgin saman kamfanin don komawa gida.

Majalisar Musulmai ta Amurka dai ta rubuta takardar koke a kan kamfanin jirgin, inda ta ce an nuna wa iyalan wariya. Lauyan Majalisar, Sana Hassan ya ce, “ Zargi a kan yadda suke mu’amala a matsayin wata barazana alama ce ta nuna wa Mista Ali da matarsa wariya kasancewar sun yi shiga irin ta Musulmi.”

Sai dai kakakin kamfanin jirgin sama na Delta Air Lines, Mista Morgan Durrant ya ce, kamfanin ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in nuna bambaci ga abokan huldarsa, ba tare da la’akari da shekarunsu ko addini ko kuma jinsinsu ba.

Ya kara da cewa kamfanin ya dukufa wajen mutunta dukkan abokan huldarsa, kuma kamfani zai gudanar da bincike tare da biyan daukacin kudin tikiti ga wadanda lamarin ya shafa.”

You may also like