Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa saura kiris ya yi murabus daga ofishinsa a lokacin da aka kaddamar da shi a matsayin shugaban kasa a watan Mayun bara bayan da ya fuskanci cewa jahohi 27 a cikin 36 ba za su iya biyan albashi ba.
Shugaban ya koka da hakan ne a jiya Alhamis yayin da yake ganawa da ‘yan makarantar koyan manufofi da dabarun gwamnati da suka ziyarce shi a fadar gwamnati.
Ya fadi yadda aka bayyana masa cewa babu komai a lalitar gwamnati a lokacin da ya tambayi ko a kawai kudaden da zai kashe.
Ya kara da cewa ya tambayi ko akwai ajiya, aka ce masa babu, babu abun da ka yi a harkar noma, wutar lantarki, da sifiri.
Buhari ya ci gaba da yin tsokaci a bangarori da dama da gwamnatin da ta gabata ta lalata al’amura a kasar, ya kuma kara jaddada matsayar sa na cewa duk wahalhalun da ake ciki a yanzu laifin gwamnatin na baya ne.
Wannan magana dai ta zo kwanaki kadan bayan da jam’iyyar APC ta amsa laifinta na kasancewa ta na da hannu a matsalar da kasar ke ciki, kuma ta yi alkawarin cewa ta dai na nunin yatsa ga gwamnatin baya.