Sauro Na Da Mutukar Amfani, Ya Kamata A Daina Kashe Shi – Farfesan Ilimin Kwari, Adeolu AndeWani farfesan ilimin kwari na jami’ar Iloro, Adeolu Ande yayi gargadi kan kisan sauro.

A wani jawabi da ya gabatar a taron da jami’ar ta shirya ranar Litinin, Ande yace akwai ilimi da yawa da ya kamata da dan Adam ya dauka daga kwari.

Yace:“ Rayuwan dan Adam ba za ta yiwu ba tare da kwari ba kuma wannan ya taimakawa rayuwan mutum kuma ya cutar da shi.

“Akan ‘yan Cututtuka irinsu rashin lafiya, asarar amfanin gona, lalacewar abinci, da sauran su wanda bai wuce kasha 5 cikin 100 ba amma mutane suna wuce gona da iri wajen kashe su.

Ande yace amfanin da suke da shi ya kunshi taimakawa girman fire, sake amfani da datti,wanda ake amfani da shi wajen kera magunguna, sinadarai da sauran su.
Yace:“ Hakikanin gaskiya shine Su kansu kwarin basu da lafiya amma suna cutar da mutane da abubuwan gona ne ba da sani ba.

“Misali shine sauro wanda ke zuwa zukar jini domin ciyar da ‘ya’yan da zata haifa.
“Manyan matan sauro suna girmama ‘yayansu sosai wanda ke sanyawa suna daukan kasadar rayuwa wajen nemawa yayansu abinci.

”Saboda haka yana da muhimmanci muyi koyi da wadannan hallitun Allah

You may also like