
Yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin takardar kudin Naira, wasu bankuna a kasar sun rufe rassansu saboda karuwar hare-hare da abokan huldarsu ke kai wa gine-ginen bankuna.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi gargadin cewa wasu kungiyoyi na shirin tayar da tarzoma a jihar saboda karancin sababbin takardun naira.
Tuni dai wasu daga cikin bankunan kasar su ka umarci wasu daga cikin ma’aikatansu su yi aiki daga gida, yayin da wasu bankuna a jihohin Legas da Ogun da Ondo da Edo suka rufe kofofin rassansu.
Ma’aikatan bankuna sun janye
A lokacin da wakilin BBC ya kai ziyara zuwa wasu bankunan kasar, ya hango babu mutane, kana babu kwastomomin da za su ciri kudi a na’urorin ATM.
Sai dai a wasu bankunan akwai ma’aikatan bankin jifa-jifa amma babu mai shiga ko fita.
Ko a jiya bankin Zenith ya rufe ofisoshinsa a jihohin Legas da Delta, kana an hango wasu ma’aikatan bankin na neman haurawa ta katanga domin gudun haduwa da fushin abokan huldarsu da suka yiwa ofishinsu kofar rago.
Matakin ya tilastawa ma’aikatan yin amfani da tsani suka haura kan katangar.
Wasu rassan bankin Zenith da ke Ikeja da Ikorodu da Agege ma dai sun kasance a rufe tun a jiya.
‘Yan Naijeriya dai na cewa tun bayan cikar wa’adin fara amfani da sabon kudi ta fara aiki ne babban bankin kasar ya rikewa harkokin kasuwancin kasar kurwasu – wani abu da watakila zai jefa miliyoyin ‘yan kasar hali na ‘ya-kwance uwa-kwance.
Za dai a iya cewa tun lokacin da aka zo da sabon tsarin fasalin naira, bankunan suka sa mu kansu cikin hali na tsaka mai wuya.
Tun a farkon makon da ya gabata, an yi ta yada wasu faya-fayan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka nuna wani mutum tsirara na kuka tare da kira ga bankin su bashi kudinsa da yayi ajiya a wurinsu.
Haka kuma an hasko wata mata tana kada jiki irin na kauraye daga ita sai rigar nono a kirjinta da kuma wandon da take sanye da shi.
Wata majiya ta ce wasu daga cikin rassan bankin da ake ganin za su iya fuskantar hari daga kwastomomi an umurci su rufe, yayin da sauran rassan da ba su da kudaden da zasu biya kwastomomi suma an bukaci su rufe su. .
Yadda yanayin yake a kudancin Najeriya
Bankuna da ke a gefen hanyar zuwa unguwar Ojodu Berger da Isheri sun rufe a ranar Talata sakamakon rashin takardun kudi da ke ci gaba da yiwa harkokin kasuwanci a kasar daurin talala.
Haka lamarin yake a wasu daga cikin bankunan Guaranty Trust, a Ojodu Berger. Za dai a iya cewa bankuna daidai ne dake a birnin Legas ne basu umarci rassansu su rufe ba. Sai dai suma suna kaffa-kaffa.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan na zuwa kwanaki kadan bayan da CBN babban bankin Naijeriya ya umurci bankunan kasar da su fara biyan mafi karancin kudi na Naira dubu 20,000 ga kwastomominsu.
Ga dukkan alamu wasu daga cikin bankunan ba su da isassun kudade na wannan adadi.
A lokacin da na ziyarci wasu bankunan na shaida tarin mutane kan layi suna jiran cire kudi daga asusun ATM. Haka lamarin yake a Egbede da Ikotun.
Wasu na’urorin ATM dai na biyan takardun kudi da basu dara dubu biyu zuwa biyar ba a rana.
A daya bangaren kuma su kansu dillalan kudi ta POS na ci gaba da karbar caji mai yawa da kuma suke biya kudi da bai dara naira 10,000 ba.
Wasu dillalan kuwa sun koma harkar sayar da katunan ‘recharge card’ wato abin nan da Hausawa ke cewa idan hagu taki sai a koma dama.