Wasu makiya addini sun sakawa masallaci wuta a garin Chateau Thierry na arewacin kasar Faransa
Jiya da safe ne wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka sakawa masallacin wuta wanda ya janyo asarar dukiyoyi.
Kungiyar hadin kan masallatai a yankin Picardie ne ta fitar da wata sanarwa inda ta la’anci wannan hari.
Sanarwar ta ce, ” a lokacin da ake muke neman hadin kai da kuma zaman lafiya a cikin kasarmu, wannan harin ya bamu mamaki. zamu yi anfani da wannan damar domin nuna goyon bayanmu ga jama’ar da ke salla a masallacin da kuma musulman yankin baki daya.”
Sanarwar ta bukaci da a gudanar da bincike akan wadanda suka kai harin domin hukuntasu kamar yadda dokar kasar ta tanadar.
Koda yake ana yaki da kyamar musulunci a kasar Faransa, kuma a cikin ‘yan shekarun nan ana ci gaba da kaiwa musulman kasar hare-hare.
Kusan mutane miliyan 5 ke rayuwa a arewacin kasar. A nahiyar Turai Faransa na cikin kasashen da musulmai suka fi yawa.