
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar dattijan arewacin Najeriya ta Northern Elders Forum ta nuna damuwa game da zargin cewa wasu ƴan siyasa sun duƙufa wajen sayen katunan zaɓe daga hannun jama’ar yankin.
Ƙungiyar ta ce sayar da katin zaɓen yana da hatsari sosai, saboda zai iya cutar da yankin.
Dr Hakeem Baba Ahmed shi ne kakakin ƙungiyar kuma ya shaida wa BBC cewa sun daɗe da samun labarin yadda ake zagayawa ana karɓar katunan zaɓen jama’a musamman mata.
Ya ce masu yin wannan abu na bijiro da wata dabara ta shawo kan mutane su ba da katinsu da sunan taimaka musu wajen shiga wani shirin yaƙi da talauci.
“Arewa ita ta fi yawan masu rajistar zaɓe, tun fil azal, musamman ma wannan zaɓen da mutane da yawa ke ta rububin ganin sun kaɗa ƙuri’a,”
“Abin da muka fahimta shi ne wata dabara ce ta rage ƙarfin masu zaɓe, kamar ni da kai muna takara, sai na je na ga inda kake da ƙarfi sai na je wurin, na sayi katuna daga hannun mutanen da na san za su jefa maka ƙuri’a.” in ji shi.
A cewarsa, wannan dabara ta ƙwace wa mutane katin zaɓensu na faruwa a kowacce jam’iyya ba wai wata jam’iyya ɗaya ba.
Dr Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa “mu a nan Arewa akwai wata dabara da ake son a yi a cuci jama’armu, katin nan haƙƙi ne kuma amana ce, kuma makami ne na yaƙin gyara a ƙasarnan,”
“Idan aka ƙwace maka kati, ai ka koma ɗan kallo, kuma idan aka gurgunta Arewa saboda rashin yawan waɗanda za su jefa ƙuri’a ai mu an cuce mu.” kamar yadda ya faɗa.
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya dai ta yi kira ga hukumomi su ƙara himma wajen magance matsalar tun kafin zaɓen ya zo gadan-gadan saboda a cewarta “abin da muka gani da abin da muke ji, da abin da bincikenmu ya nuna, ba ƙaramar ɓarna, wannan abin zai yi ba.”
‘Doka za ta yi aiki kan masu laifin zaɓe’
Asalin hoton, Getty Images
Sai dai a yayin da wannan ƙungiya ke neman hukumomi su ɗauki matakan yaƙi da wannan matsala ta sayen ƙuri’u, hukumomin tsaro a jihar Kano, ɗaya daga cikin jihohin arewa sun ce sun tsyaa kai da fata domin tabbatar da ganin doka ta yi aikinta a kan duk wanda aka samu yana aikata ba daidai ba.
Rundunar ƴan sandan jihar ta ce duk mutumin da aka samu da laifin tayar da zaune tsaye lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma a lokacin zaɓe, to zai girbi abin da ya shuka.
Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar, Dauda Mamman ya faɗa wa BBC cewa a baya-bayan nan sun tattauna da masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe inda ya ce a taron sun ja hankalin ƴan siyasa kan amfani da ƴan banga saboda illar hakan ga zaman lafiya.
Rundunar ta ce nan gaba za su shirya wani babban taron masu ruwa da tsaki inda za su ja hankalin ƴan siyasa tare da sanya hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya yayin zaɓen da kuma bayan gudanar da shi.
Asalin hoton, Kano Police Command Facebook
Ya ce “Ciyamomi da sakatarori da ƴan takara, za mu gayyace su da ƙungiyoyi masu zaman kansu da duk masu ruwa da tsaki don mu tattauna kan waɗannan matsaloli ta yadda za mu jaddada wa ƴan siyasa cewa ba za mu yarda da wannan ta’addanci ba.”
Ya ƙara da cewa “a lokacin za mu rubuta yarjejeniya, za mu sanya su, su sa hannu kan yarjejeniya, yarjejeniyar kuma da za mu rubuta za mu ɗebo ne har daga cikin sashen dokar Penal Code inda matuƙar ka bar mutum yana bin ka, yana yawo da makami, ka zama mai taimaka wa mai laifi, duk laifin da ya aikata su za mu riƙe,”
“Muna son kuma duk wanda muka kama muna da ƙudurin mu samu atoni janar ba maganar a yi masa tara, mun fi son a ajiye shi a gidan yari , ya zauna har bayan zaɓen.”