Scholz: Zargin badakalar kudi | Labarai | DWHakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ke kokarin wanke kanshi daga shakkun da ake da shi na rawar da ya taka a badakalar kudaden haraji.

Scholz zai ba da shaida a karo na biyu ga kwamitin majalisar dokoki a Hamburg, wanda ke binciken ko ’yan siyasan kasar sun taimaka wa banki don kaucewa mayar da kudin harajin na bogi. Shugaba Scholz dai ya kasance magajin garin Hamburg daga shekarar 2011 zuwa 2018 kafin ya zama ministan kudi na gwamnatin tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
 You may also like